Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen
Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu
Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa
Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar
Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kayan Ball A Jikinsa Kuma Ga Wayoyinsa Kwaya Biyu Note 10 Samsung Da Kuma Wata Karamar Waya Itel Kuma Babu Aljihu A Jikinsa Sai Ya Bata Ajiya Har A Lokacin Ake Ta Yi Masa Wasa A Lokacin Ne Sai Mai Gidansa Da Suka Je Wajen Ya Kirashi A Waya Yace Sauko Kasa Don Su Tafi Yama Saukowa Kasa Sai Ya Tono Da Wayoyinsa Sai Ya Koma Yace Mata Ta Bashi Wayarnan Abu Kamar Wasai Sai Tace Bata Wajenta
Haka Akayi Tayi Taki Fito Masha Da Ita Inda Da Safe Kuma Yake Rahotanta Wajen Yan Sanda Don Ta Fito Masha Da Wayoyinsa Amma Taki Amsa Laifin Ita Ta Dauki Wayoyin Nasa
Magwadal Ya Tafi Gida Kafin Ya Dawo Kuma Sai Ji Labarin Yayi Ance Ahmad Musa Yazo Yayi Belin Dinta An Saketa Inda Yan Sanda Suka Ce Masa In Har Yana So Aje Gidansu Su Madam Korede Don Yin Bincike Sai Ya Cike Wani Form An Bashi Izini Shi Kuma Wannan Form Din Ana Kashe Kudi Kafin A Baka Shi ,Madagwal Kuma Gari Yaci Wuta Bashi Da Da Kudin Biyan Wannan Form
Jarumin Barkwanchin Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Yake Kararta Wajen Yansanda Inda Ya Bayyana Cewar Sun Taba Samun Matsala Ne Da Wani Saurayinta A Don Haka Yake Zargin Ta Sace Masa Waya Ne Don Su Bata Masa Social Midiya Dinsa Dake Kan Wayar Tasa Domin Ana Iya Amfanin Da Social Midiya Din Celebrate Wajen Damfarar Mutane
Sannan Ya Bayyana Rashin Jin Dadin Yadda Ahmad Musa Yayi Belin Din Madam Korede Ba Tare A Kiranshi Ba An Bi Masa Hanginsa Na Matsata Ta Fito Masa Da Wayar Tasa Ba Kadai Kadan Daga Cikin Bidiyan Yadda Suka Zaman Nasu Har Aka Sami Damar Sace Masa Wayar Tasa
Da Fatan Allah Ya Bayyana Wadda Ya Sace Masa Wayar Tasa Ameen A Wani Bangaren Kuma Na Daban Gfresh Ya Mayar Da Martanin Kan Sadiya Haruna Da Tayi Kirarin Bashi Da Lapiya A Wajen Kwanciyar Gado Da Iyali
Sadiya Haruna Ta Fadi Hakan Ne A Lokacin Da Ake Tattauna Da Ita Da Gidan Talabijin Na Hadiza Gabon Inda Tace Da Fari Gfresh Yaronta Ne Kuma Bata Taba Tsamani Zata Iya Aurensa Ba Amma Kaddarar Tasa Hakan Ya Faru
Tace G Fresh Bashi Da Lapia A Zamantakewar Aure Inda A Ranar Da Zasu Fara Zama A Daki Daya Na Aure Sai Taga Ashe Yana Da Matsala Har Ta Kira Wani Mai Gidanta Yace Zai Bashi Maganin Amma A Bangaren G Fresh Da Yaji Wannan Bayanin Ya Karyata Wannan Batun Kamar Yadda Zakuga Bidiyan
To Allah Ya Kyauta..
Comments
Post a Comment