Abubuwan Da Suke Janyo Jin Zafi Yayin Saduwa Da Iyali Da Ya Kamata Ku Sani Domin Magance Matsalar
- Get link
- X
- Other Apps
Wannan jin zafi yayin saduwa kan haddasa saɓani da matsalolin rayuwar aure..bayan jin zafi lokacin saduwa akan kuma samu zafi a zuci, wato rashin jin daɗi saboda wannan matsalar ta rashin samin gamsasshiyar rayuwar aure. Maza za su iya samun matsalar kamar yadda mata ma za su iya samu.
Meke kawo Jin zafi lokacin saduwa?
1. Bushewar gaba
Babban abinda ke kawo wannan matsalar ta jin zafi lokacin saduwa shi ne bushewar farji ko ɗaukewar ni'ima. Maganin wannan shi ne amfani da mayuka da za su sa wajen yayi danshi kafin sabuwar. Yawan shan ruwa da gabatar wasa shi ma ya Kan taimaka.
2.Saduwa bayan haihuwa
Saduwa bayan haihuwa ba tare da bayar da tazarar lokaci ba kan janyo wannan matsala
3.Sanyin Mahaifa ko Mafitsara
Kasancewar ƙwayar cuta a farji kan iya janyo sanyi na mahaifa Dana mafitsara wanda suna daga cikin abubuwan dake janyo jin zafi lokacin saduwa
4. Tunanin cewa za'aji zafin saduwa tunkafin a sadu
Tunanin cewa za a ji zafi lokacin saduwa (tun kafin a sadun) kan sa tsokar da ke sarrafa farji ta suke, hakan zai haddasa jin zafi yayin saduwa.
5. Matsaloli na cikin mahaifa
Matsalolin mahaifa irin su tsiro acikin mahaifa(fibroid) da da wasu matsaloli na mahaifa kamar "endometriosis" kan iya janyo wannan matsalar
6. Ciwon sanyi (gonoriya a maza) a maza
Yakanzo da Jin zafi lokacin fitsari,fitar farin ruwa ta gaba da dai sauransu,ana daukarsa ne ta hanyar saduwa.
7. Kumburi ko sanyin prostrate(Prostatitis) a Maza
Yakanzo da zafin fitsari da Jin ciwo a dubura,ko Yawan fita yin fitsari bayan Jin zafi lokacin saduwa a maza
Ire- irensa
A. Jin zafi a farkon farji:
da zarar kan azzakarin namiji ya ɓuya cikin farji, sai mace ta fara jin zafi. Abubuwan dake kawo hakan sun haɗa da bushewar gaba, wani ciwo a wajen, ko kasancewar ƙwayar cuta a wajen.
B. Jin zafi a can cikin farji:
ana jin wannan zafi ne bayan al'aurar namiji ta shiga gaba daya. Abinda ke kawo wannan zafi ya haɗar da : tsohuwar tiyata ko aiki da aka taɓa yiwa mutum, ko matsaloli na cikin mahaifa kamar yadda muka ambata
Magani
Magani ya danganta da abunda ke kawo shi sannan a asibiti akeyinsa.likita zaiyi gwaje gwaje ta hanyar aune aune da tambayoyi.
1. Idan mace mai ciki ce, ana iya jinkirta saduwa sai bayan ta haife da wata ɗaya da rabi
2. Idan bushewar farji ce, za a iya amfani da mayukan da za su iya kawo danshi a wajen kamar irinsu oestrogen vaginal creams
3. Idan kuma mace ta wuce shekarun ɗaukar ciki, juma ta na gama da bushewar gaba, akwai buƙatar ta ga likita da ya bata magani na musamman
4. Za ku iya sauya salon kwanciya wanda ba za a ji zafi ba a lokacin da ake saduwar
5. Zuwa ganin likitan jima'i (sex therapist) domin Bada shawarwari
- Get link
- X
- Other Apps

Comments
Post a Comment