Hakika albasa na da tsohon tarihi duba da yadda al'umma ke amfani da ita a harkokin abincinsu da kuma magani.
Play ▶️
Masana sun yi ittifakin cewa albasa na da wasu muhimmman sanadarai da ke taimaka wa wajen gina jikin dan-adam, baya ga haka sanadaran da albasa ke kunshe da su na da tasiri kan wasu cututtukan jiki.
Play ▶️
Shekaru da yawa da su ka shude, al'ummomin Duniya daban-daban ke amfani da albasa don magance cututtukan da ke damun su, kamar ciwon sanyin kashi, mura, ciwon makogoro da gabobi da sauran su.
Play ▶️
Ganin yadda albasa ke da amfani ga lafiyar dan- adam mu ka dacewar yin bincike don zakulowa ma'abota wannan shafi, fa'idojin albasa, kuma mun yi wannan makala lakabi da 'Amfanin albasa ga lafiyar Biladama. A sha karatu lafiya.
1. Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro.
Daga cikin amfanin albasa ga dan-adam akwai maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro. Duk wanda ke fama da daya ko duk ciwon da muka zana a sama, musamman wanda ke farma da tari ko mura mai tsanani, ya nemi man Albasa cikin babban cokali 9, da zuna babban cokali 9, sai ya zuba man albasar cikin zumar ya gauraya sosai,daga nan sai ya samu mazubinsa mai tsafta kuma mai murfi ya adana ya arika shan cokali uku a kullum, wato safe, rana da dare.
2. Maganin Zafin Fitsari. Ana amfani da albasa don magance matsalar fitar fitsari da zafi. Ga mutumin da ke shan wahala wajen fitar fitsari, ya nemi man albasa ya hada da zuma mai kyau da lemon tsami ya gauraya, ya tabbatar sun gaurayu sosai, sai ya dinga sha sau biyu a rana, ma'ana da safe da yamma, sannan kuma ya rika shafa man albasa ajikin mararsa.
3. Maganin Sanyin Kashi
Albasa na maganin sanyin kashi. Duk mai fama da wannan matsala ta sanyin kashi , sai ya samu albasa ya dafa Albasa ya dafa ta, ya zuba man zaitun a rika dumama wajen da ya ke jin ciwon, sannan da dare kafin ya kwanta barci sai ya shafe wajen ciwon da wannan hadin, sannan kuma ya rinka sha da safe, haka za ayi har tsawon kwana bakwai. In sha Allahu za'a dace.
4. Maganin Maruru Ko Kuraje. Hakanan, daga amfanin albasa ga lafiyarmu, har da maganin kuraje ko maruru. Yadda za a yi shine, a samu albasa a kirba ta, sai a hada da man zaitun a dafa ake wanke marurun ko kurajen, bayan an karmmala wanke wa, sai a shafa man zaitun a gurin.
5. Maganin Zubar Gashi.
Ina matan da ke fama da zubar gashi? Sai mu ce kayanku ya tsinke a gindin kaba, saboda za ku iya yin amfani da albasa domin magance wannan
matsala. Duk matar da ke fama da zubewar
gashi, ta samu ruwan albasa, ta hada da man
Simsim, da kuma garin Baqadunas, ta dinga
shafewa kanta da shi, ta tabbatar ta game kanta
tun daga matsirar gashinta. Za ta yi haka a
kulum kafin ta kwanta barci. Idan gari ya waye
sai ta wanke da ruwan dumi. Haka za ta yi har
tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji za ta
samu biyan bukata.
6. Maganin Lagwada.
Amfanin albasa ga lafiyar dan-adam ya hada da
tasirinta wajen maganin kurajen lagwada, idan
mutum na fama da wannan matsala, sai ya samu
ruwan albasa ya hada shi da ruwan Kahl a saka a
wajen a daure sai bayan kwana daya ko biyu sai
a kwance idan bata cire ba sai a maimaita har sai
ta cire. Allah Ya sa mu dace,amin.
7. Magarnin Karfin Mazakuta.
Masana sun nuna cewa, daga cikin amfanin
albasa ga lafiyarmu, akwai maganin karfin maza.
Ga mai son ya amfana da wannan fa'ida ta
albasa sai ya samu kofi daya na ruwan zuma mai
kyau, marar hadi da rabin kofi na ruwan albasa,
sai ya zuba cikin tukunya ya dora kan wuta idan
ya fara tururi sai ya sauke sai a rinka shan
babban cokali daya sau 3 a kullum.
8. Maganin Amosanin Ka.
Harilayau daga cikin amfanin albasa ga lafiyar
dan adam, har da maganin amosanin ka, duk
matumin da ke fama da amosanin ka, sai ya
samu ruwan albasa, ya hada da man Simsim, da
kuma garin Baqadunas, ya dinga shafewa kansa
da shi, ya tabbatar ya game kansa tun daga
matsirar gashi. Zai yi haka a kullum kafin ya
kwanta barci. Idan gari ya waye sai ya wanke da
ruwan dumi. Haka zai yi har tsawon mako guda.
Da yardar Ubangiji zai samu biyan bukata.
9. Maganin Daji (Cancer) Na Fata
.
Ana yin amfani da albasa wajen maganin ciwon
dajin fata. ldan mutum ya na fama da wannan
matsala sai ya samu ruwan albasa, da garin
hulba da karamin cokali na farar wuta. Zai hada
ruwan albasar da garin hulba da kuma farar
wutar waje guda ya gauraya su, sai ya ke
shafawa a wajen ciwon safe da yamma tsawon
mako biyu.
10. Albasa Na Taimaka Wa Ma Su Ciwon Sikila.
Daga cikin irin amfanin albasa ga lafiyar bil
adama, akwai taimaka wa ma su fama da cutar
sikila. ldan mutum na fama da wannan matsala
ta sikila sai ya rika yanka albasa tare da ganyen
Zogale yana ci. Insha Allahu, zai samu saukin
ciwon Sikila din.
Comments
Post a Comment