Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Idan har kasan kana da irin wadannanmatsalolin to kada kansake kayi aure

Shi dai aure ibada ne. A cikin sa akwai dadi akwai kuna wahala. Wani lokacin yana zuwa da jarabawa kamar dai yadda sauran aiyuka na ibada suke.
Wasu suna yiwa aure fahimta na daban, wasu ma auren suke ba tare da sun fahimce shi auren ba.

PLAY ▶️

Akwai kuma masu yiwa auren wani irin kallon.Wanda da wannan kallon suke shiga harkar aure har ma suyi. Irin wadannan maza ne ko mata, basa jimawa cikin auren sai su rabu.

PLAY ▶️

Don haka muddin kana yiwa aure irin wannann kallon ko kana sone kayi aure saboda wadannan dalilan to gara ma kada kayi.

1: Wasu suna yin aure ne saboda sun ga abokansu ko wasu na kusa da sun yi. Hakan yasa suma sai kawai suyi.

Duk wanda zai yi aure da irin wannan tunanin ba tare da ya shirya ba zai iya fuskantar matsala a nan gaba.

2: Saboda Suruntu mutane wasu sai kawai su ce zasu yi aure. Kada ka bari surutun masu surutu ya tunzura yin aure baka shirya ba. 

Domin su wadannan da suke surutun sune kuma zasu ci gaba da wani surutun na ka kasa rike matar.

Don haka aure Kada ka yi shi sai ka shirya masa.

3: Wasu kuma na yin aure ne da tunanin zasu hole. Sam aure ya wuce wannan. Domin akwai holewa akwai kuma horarwa. Don haka ka shirya wa dukkannin su muddin kana son zaman aurenka ya inganta.

4: Wasu suna yin aure ne saboda tsaro. Irin wadannan mutane musamman ma mazajen da suke zuwa wasu karshen Turai su zauna.

Sai su samu 'yar kasa su aure ba saboda Allah ba sai domin garkuwa da ita wajen samun takardun zama a Kasar. Bayan wani dan lokacin da samun biyan bukata sai kuma su nemi raba auren ko u bace ma a daina ganin su.

Wadannan yalayen ba wai ya tsaya ga maza kadai ba. Har mata suna yin aure saboda irin wadannan dalilan daga bisani ko dai su zauna cikin azabar miji ko kuma su kasa hakuri su fito.

Abunda ya kamata kowa ya gane aure ba ayinsa da wasa ko kuma da garaje.

Comments

Popular posts from this blog

Ankai Sheikh Aminu Daurawa Bango Yayi Murabus Daga Kan Shugaban Hukumar Hisbah Na Jihar Kano