Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Wasu Kurakurai 8 Da Matan Aure Keyi Har Yayi Sanadin Mijinsu Ya Auri Yar Aikin Gidansa

Ba sabon abu bane aji cewa' yar aiki ta aure maigida ko kuma ta kori uwar gidan ma gaba daya.

PLAY ▶️

Wannan matsalar yana faruwa ba tun yanzu ba. Wanda kuma har wannan lokacin wasu matan sun kasa ganewa sune ke jawo hakan da kansu har abun yazo kuma ya damesu.

Mafi yawan mazaje sun fi son 'yar aiki mace ta kula da aiyukan cikin gida maimakon namiji saboda da dalilai na tsaro. Wasu matan kuma sun gwammace namiji yayi musu aiyukan gidan domin gudun kada su kawo wacce zata iya musu illa. 

Amma da yake maza sun fi karfin su a daukar matsayi hakan yasa wasu matan suke saduda amma ba domin suna so ba.
PLAY ▶️
Sai dai kuma matan ke jawo matsalar da suke fuskanta da 'yan aikin su da kansu. Domin sune suke zaban wacce zata musu aikin ba Mazajen su ba.

Ga wasu kurakuren da mata suke yi har yan aikin su ke zama kishiyoin su.

1: DAUKO WACCE TA FITA WAYO:-Mata da dama idan sun tashi dauko' yar aiki a rashin sani sai su dauko macen data fisu wayo a badini amma a zahiri tayi kama da doluwa.

Irin wadannan matan basa yadda su fito da fiskarr kyaun su na asali idan zasu je neman aiki.

 Sai suyi biji biji yadda mace idan ta ganta tamkar wata abar tausayi. Amma da zaran ta saki jiki zata soma fito da Halittun ta yadda duk wanda ya ganta zai kyasa.

2:- SAKA SU AIYUKA NA MUSAMMAN: Akwai wasu aiyukan da duk rashin son aikin mace ita ya kamata ta yiwa mijin ta shi amma ba ta saka wata ta yi masa ba muddin dai ba yar cikinsa bane.

Aiyuka irin na gyaran dakin miji. Yiwa miji girki fita da miji sayayya duk bai dace mace ta bari 'yar aikinta ta ke mata ba.

3:- BARIN YAR AIKI TA FAHIMCI MATSALARKI DA MIJINKI:- Muddin zaku bari' yar aiki tana fahimtar abunda yake hadaki da mijinki sabani to tabbas zata iya amfani da wannan damar ita kuma ta rika daɗada masa da abun, yadda har zai soma sha'awar inama itace Matarsa. Don haka ki kiyaye hira da yar aiki akan matsalolin ki da mijinki.

4:- SAKA SUTURAN DA ZAI FITO DA SURAR TA: Kada ki ji kunyar taka mata burki muddin kika fahimci cewa 'yar aikin ki tana son rika shiga irin wanda zai rika fito da Surar ta a gaban mijinki.

Ana iya samun wani wasu Halittun ta da suka fi naki da magida zai iya sha'awar su wanda hakan zai zama tarkon da zata kamashi da su.

5:-.DAUKAR' YAR AIKIN DATA FIKI KYAU: duk kuwa da namiji a wani lokacin ba kyaun mace bane a gaban sa ba. Amma daukan yar aikin data fiki kyau tamkar kin Gayyatowa kanki matsala ne da kanki.

 Gara dai wacce kika fi kyau koda wani abu ya kasance za a zarge shi amma ba ke ba

.
6:- BAIWA 'YAR AIKIN DAMAR KAWAI MIJINKI ABINCI: Cikin Sauki' yar aikin da take son aure miki miji zata iya amfani da wannan damar domin ganin ta ciyar dashi wani shirin da zata iya juya masa kansa ya ji ita yake so.

7:- WULAKANTA BAKI A GABAN TA: Idan kina wulakanta bakin mijinki a gaban yar aikin ki Ita kuma zata yi amfani da wannan damar wajen kyautata musu har ta shiga ransu. Hakan kuma zai bata damar samun shiga wajen mijinki cikin sauki ta hanyar wadannan da kike wulakanta wa ita kuma tana daðaɗa musu.

8:- WANKE MASA KANANAN WANDUNANSA:- Akwai wani sirri na musamman a wanke kananan wanduna. Duk ma'auratan da suke wanke wa juna kananan wandunansu soyayya da kauna na musamman yana kara shiga tsakanin su. Don haka idan kika bar 'yar aikin ki ita ke wanke masa kuma ta goge masa sai aji a ranta inama itace abunda ke adana wandon nan yake shiganta. Don haka ki kiyaye.

9:- BATA DAMAR YIN HIRA DA MIJINKI:-Idan kika baiwa yar aiki mai wayo damar yin hira da mijinki cikin sauki zata iya aure miki miji. Domin zata iya amfani da Kalaman data san baki masa domin jawo hankalinsa.

10:-RASHIN BAIWA MIJI LOKACI: Idan kin kasance irin matan nan ne da suka damu da harkokin gabansu amma basu damu da kula da miji ba to a kwana a tashi zaki tsinci kanki cikin matan da 'yar aiki ta aure Mazajen su.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba