Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Abubuwa Biyar Da Sukae Jan Hankalin Mace A Tattare Da Namiji

Mata suna da banbanci hakazalika maza. Babu wani abu da ake amfani dashi wajen gwajin namiji mai nagarta. Wasu na duba irin ingantacciyar rayuwa ne inda wasu kuwa suna kallon rayuwa mai cike wadata. Amma wasu matan da yawa sun amince da wadannan halayen ko abubuwan da suke matukar son a tattare da namiji. 

1. Sanya annashuwa Duk mutumin da zai sa mace cikin annashuwa zai iya janye hankalinta tare da dasa soyayyarsa a zuciyarta. Kowa na da bukatar abokin zama mai saka shi cikin farin ciki koda kuwa ana cikin halin jarabawa. 

2. Saukin kai da kula Ba sai mutum ya tseratar da mutane yayin gobara bane za a kira shi da mai saukin kai a cikin jama'a ba. Namiji mai saukin kai da kula na iya sanya mace ta fada son shi ba kadan ba. A lokutan da damuwa ta samu mace, tana bukatar namiji mai kula a tare da ita. 

3. Gaskiya Babu mai son makaryaci. Gaskiya kuwa babbar nagarta ce a tattare da namiji. Namiji mai gaskiya shine wanda zai iya sanar dake gaskiyar lamari ba tare da cin amana ba. Gaskiya da biyayya a hade suka. 
4. Soyayyar gaskiya Namiji mai iya nuna wa mace soyayya a koyaushe yana iya tafiya da zuciyarta. Akwai hanyoyin bayyana soyayya masu tarin yawa. Budewa mace kofar gida ko ta mota, rike mata hannu yayin tsallake titi ko kuna shawagi. Kananan abubuwa ne dai ke bayyana tsantsar soyayya. 

5. Nuna wa mace ita ta musamman ce Mata da yawa na son namiji ya nuna musu sun kasance na musamman. Yabawa mace kwalliya, girki ko wani kokari da tayi don birgeka na kara mata soyayyar namiji. Duk namijin da ke nuna wa mace ita ta dabance na samun matsuguni mai girma a zuciyarta. 

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba