Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

ABUBUWAN DA MAZA KE SO A JIKIN MATAN DA SUKE SO

Idan Namiji ya faɗa Soyayya da mace, akwai wasu abubuwa da yawa ƙanana game da ita da suke saka shi Murmushi bawai kawai a fuskar shi ba, har Zuciyar shi.

1. Duk lokacin da namiji ya tina dake yana yin Murmushi indai yana sonki. Koda yana aiki ne, koda Yana ciki Damuwa ne, daya tina ki sai yaji ya wuce. Idan har Namiji na son mace kuma yayi Sa'ar Mace, koda basa tare Zaina farin ciki idan ya tina irin Halayyar da take nuna mishi

2. YANA SON YAGA YA SAKA KI MURMUSHI

Kin taba kula cewa idan na miji yaga kinyi Murmushi shima yana yi? Idan namiji mai abun dariya ne yakan yi iya bakin ƙoƙarin shi domin yaga kinyi Murmushi, dariya, dakuma Baki lokacin shi. Kuma yana son ace shine yasa kikai wannan farin cikin.

3. YANA SON KASANCEWA A KUSA DAKE. 

Idan namiji na son ki, zakiga koda a cikin mutane ne zaina son zama kusa dake, yana son koda yaushe ki kasance tare dashi. Yana gina shauƙi sosai kasancewa kusa da wanda kake so.

4. YANA SO KIYI MURMUSHI BAYAN YA SUNBACE KI. 

Sunbata Nada tasiri Sosai a Soyayya, kuma wata hanya ce da take da saurin isar da saƙon Zuciya zuwa ga zuciya.

5. YANA SON YANA KAMAKI KINA KALLON SHI.

Kowa yana son ana sonshi, ana Ririta shi. Yaji cewa shima fa akwai wacce take ji dashi. Idan kina yawan kallon Namiji zaisa yaji yana ƙara ƙaunar ki sosai, sannan zaina yawan yi miki abunda kike so batare da kin tambaya ba.

Idan muna tare da mace wacce take matuƙar so ta zauna damu wacce take mana Soyayya irin wacce muke mata, wacce take bamu farin ciki, yarda, aminci, da Soyayya kamar yadda muke mata, babu abunda zaka nema ga mace kamar Haka a duniya.

6. YANA SON YAGA KINA YIN WANI ABUN DARIYA DA BAKI SAN KINA YI BA.

Misali: kina Murmushi har dimple naki ya bayyana, ko kina Rufe fuska idan ya baki dariya, yawan jin kunya, ko wata magana da kike acikin zance da yake son Yana jin haka. 

Wasu mazan ma har So Suke suna Tsokanan Mace Idan suna son Tana yi musu irin wannan Abunda dan kawai suji daɗi.
7. YANA SON KINA GIRMAMA SHAWARIN SHI.

Idan Namiji ya fahimci cewa kina Girmama Shawarin shi idan ya baki yana ƙara mishi shauƙin sonki Sosai. Domin ɗaya daga cikin daɗin zama shine Girmama ƙudurin juna, musamman ta fuskar Halayya.

Sannan Kina neman Shawarin shi, kina yawan Tambayar shi menene tinanin shi akan abu kaza. Idan namiji yana yawan baki shawari shima zaina Tambayar ki shawari, kuma duk irin wacce kika bashi zai ɗauketa da muhimmanci

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba