Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Abubuwan Dake Sa 'Yan-Mata Raina Samari

Samari sai ku maida hankali akan wasu abubuwa da zasu jawo muku girma a wajen ‘yan matan ku. Sau da dama matasa kan shiga runbun soyayya da har sukan aikata wasu abubuwa ga ‘yan mata batare da suna cikin hayyacin suba.

Wadansu abubuwa da samari kanyi ma ‘yan matan su, da suke ganin kamar suna burge ‘yan matan, amma su ‘yan matan suna ganin samari kamar basu san abun da su keyi ba. Kada zafin soyayya ya kwashe saurayi ya biyama budurwa kudin makaranta, ba’ana nufin kada mutun ya nuna son shi da kauna ga mace da kuma harkar karatun ta. Sau da yawa samari kan kashe kudi a kan mace, sai ta gama karatu sai ta watsar da shi ta kama wani sabon saurayin.

Kada ka siya wasu kaya masu tsada don burge budurwa, bayan tasan baka da karfin siyan kayan, zata rainaka idan ta gane cewar bashi ka siyo kayan, haka kada saurayi yayi zamba cikin aminci duk dan ya samu kudin da zai burge budurwa. Hakan zai kara saka shi cikin halin wahala idan budurwar ta yarda shi.
Kada kayi fada akan budurwa, ko saurayi ya rabu da aboki saboda budurwa, tace bata son abokin ko rashin kyautatawa tsakanin ka da wasu akan budurwa, shima kuskure ne. Haka kada budurwa tasa saurayi canza surar jikin shi, ko dai tace batason yadda gashin kanshi yake, ko tanason taga yayi wani abu da zai sa shi cikin wani hali na damuwa daga baya.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba