Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Amfanin Albasa guda 10 ga lafiyar dan adam da ya kamata ku sani

Amfanin Albasa guda 10 ga lafiyar dan adam da ya kamata ku sani

Hakika albasa na da tsohon tarihi duba da yadda al’umma ke amfani da ita a harkokin abincinsu da kuma magani. Masana sun yi ittifakin cewa albasa na da wasu muhimmman sanadarai da ke taimaka wa wajen gina jikin dan-adam, baya ga haka sanadaran da albasa ke kunshe da su na da tasiri kan wasu cututtukan jiki.

Shekaru da yawa da su ka shude, al’ummomin Duniya daban-daban ke amfani da albasa don magance cututtukan da ke damun su, kamar ciwon sanyin kashi, mura, ciwon makogoro da gabobi da sauran su.

Ganin yadda albasa ke da amfani ga lafiyar dan-adam mu ka dacewar yin bincike don zakulowa ma’abota wannan shafi, fa’idojin albasa, kuma mun yi wannan makala lakabi da “Amfanin albasa ga lafiyar Bil-adama. A sha karatu lafiya.

1. Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro.
Daga cikin amfanin albasa ga dan-adam akwai maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro. Duk wanda ke fama da daya ko duk ciwon da muka zana a sama, musamman wanda ke fama da tari ko mura mai tsanani, ya nemi man Albasa cikin babban cokali 9, da zuma babban cokali 9, sai ya zuba man albasar cikin zumar ya gauraya sosai, daga nan sai ya samu mazubinsa mai tsafta kuma mai murfi ya adana ya arika shan cokali uku a kullum, wato safe, rana da dare.

2. Maganin Zafin Fitsari.
PLAY ▶️

Ana amfani da albasa don magance matsalar fitar fitsari da zafi. Ga mutumin da ke shan wahala wajen fitar fitsari, ya nemi man albasa ya  hada da zuma mai kyau da lemon tsami ya gauraya, ya tabbatar sun gaurayu sosai, sai ya dinga sha sau biyu a rana, ma’ana da safe da yamma, sannan kuma ya rika shafa man albasa ajikin mararsa.
3. Maganin Sanyin Kashi

Albasa na maganin sanyin kashi. Duk mai fama da wannan matsala ta sanyin kashi , sai ya samu albasa ya dafa Albasa ya dafa ta, ya  zuba man zaitun a rika dumama wajen da ya ke jin ciwon, sannan da dare kafin ya kwanta barci sai ya shafe wajen ciwon da wannan hadin, sannan kuma ya rinka sha da safe, haka za ayi har tsawon kwana bakwai. In sha Allahu za’a dace.

4. Maganin Maruru Ko Kuraje.

Hakanan, daga amfanin albasa ga lafiyarmu, har da maganin kuraje ko maruru. Yadda za a yi shine, a samu albasa a kirba ta, sai a hada da man zaitun a dafa ake wanke marurun ko kurajen, bayan an kammala wanke wa, sai a shafa man zaitun a gurin.

5. Maganin Zubar Gashi.

Ina matan da ke fama da zubar gashi? Sai mu ce kayanku ya tsinke a gindin kaba, saboda za ku iya yin amfani da albasa domin  magance wannan matsala. Duk matar da ke fama da zubewar gashi, ta samu ruwan albasa, ta hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ta dinga shafewa kanta da shi, ta tabbatar ta game kanta tun daga matsirar gashinta. Za ta yi haka a kullum kafin ta kwanta barci. Idan gari ya waye sai ta wanke da ruwan dumi. Haka za ta yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji za ta samu biyan bukata.

6. Maganin Lagwada.

Amfanin albasa ga lafiyar dan-adam ya hada da tasirinta wajen maganin kurajen lagwada, idan mutum na fama da wannan matsala, sai ya samu ruwan albasa ya hada shi da ruwan Kahl a saka a wajen a daure sai bayan kwana daya ko biyu sai a kwance idan bata cire ba sai a maimaita har sai ta cire. Allah Ya sa mu dace,amin.

7. Maganin Karfin Mazakuta.

Masana sun nuna cewa, daga cikin amfanin albasa ga lafiyarmu, akwai maganin karfin maza. Ga mai son ya amfana da wannan fa’ida ta albasa sai ya samu kofi daya na ruwan zuma mai kyau, marar hadi da rabin kofi na ruwan albasa, sai ya zuba cikin tukunya ya dora kan wuta idan ya fara tururi sai ya sauke sai a rinka shan babban cokali daya sau 3 a kullum.

8. Maganin Amosanin Ka.

Har-ila-yau daga cikin amfanin albasa ga lafiyar dan adam, har da maganin amosanin ka, duk matumin da ke fama da amosanin ka, sai ya samu ruwan albasa, ya hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ya dinga shafewa kansa da shi, ya tabbatar ya game kansa tun daga matsirar gashi. Zai yi haka a kullum kafin ya kwanta barci. Idan gari ya waye sai ya wanke da ruwan dumi. Haka zai yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji zai samu biyan bukata.

9. Maganin Daji (Cancer) Na Fata.

Ana yin amfani da albasa wajen maganin ciwon dajin fata. Idan mutum ya na fama da wannan matsala sai ya samu ruwan albasa, da garin hulba da karamin cokali na farar wuta. Zai hada ruwan albasar da garin hulba da kuma farar wutar waje guda ya gauraya su, sai ya ke shafawa a wajen ciwon safe da yamma tsawon mako biyu.

10.  Albasa Na Taimaka Wa Ma Su Ciwon Sikila.

Daga cikin irin amfanin albasa ga lafiyar bil adama, akwai taimaka wa ma su fama da cutar sikila. Idan mutum na fama da wannan matsala ta sikila sai ya rika yanka albasa tare da ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu, zai samu saukin ciwon Sikila din.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba