Bidiyan Yadda Magoya Bayan Juyin Mulki Nijar Ke Cina Wuta A Ofishin Jakadanchin Faransa A Niamey
- Get link
- X
- Other Apps
A yanzun nan sabuwar Gwamnatin sojojin kasar Nijar ta nemi agajin gaggawa daga kasar Ra*sha, tare da neman kasar Far*ansa da sauran kasashen Yamma da ke kasar da su tattara su fice daga kasar Nijar cikin gaggawa.
A yanzu haka kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Bola Tinubu, suna gudanar da zama na musamman a Abuja, don bin hanyoyin da suka dace na ganin sun dawowa da Bazoum mulkin kasar, inda har suka bawa sojojin kasar wa’adin sati guda domin su gaggauta dawo da mulkin kasar, kamar yadda suka same shi.
Akwai abunda ya kamata mu kara lura sosai musamman a wurin zanga-zangar masu goyon bayan sojojin kasar da suka gudanar a yau, za kuga talakawan kasar rike da tutotin kasar Ra*sha sannan suna rike da allunan kira ga sojojin kasar da, kada su yarda su kara aminta da kasar Far*ansa.
Hakika hankalina ya fara karkata akan lallai sojojin kasar Nijar da suka yi juyin mulki ba suda alaka da kasar Far*ansa, domin koda wasan kwaikwayo ne suke yi mana to lamarin da bazaika haka ba, musammanma yadda naga talakawan kasar masu yawan gaske suke fitowa suna bata lokacin su wurin gudanar da zanga-zangan nuna goyon baya a gare su.
PLAY ▶️Lallai ya zamar mana dole mu cigaba da yiwa al-ummar Nijar Addu’a, wata kila wannan juyin mulkin ya zama irin na kasar Ma*li.
- Get link
- X
- Other Apps
Comments
Post a Comment