Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Dalilin Da Yasa Naki Tayin Karba Albashi N20m Duk Wata A Jami'ar Na Zauna A BUK

Tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC), Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya bayyana yadda ya ki amincewa da tayin da wata jami’a ta yi masa na Naira miliyan 20 duk wata 
Rasheed, wanda tsohon shugaban jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ne a makon jiya ya sanar da yin murabus daga NUC da radin kansa, shekaru uku kafin cikar wa’adinsa. 
Ya fada a fili cewa, burinsa shi ne ya ci gaba da karantarwa a BUK, kamar yadda jaridar Daily Trust a karshen mako. 

Ya kasance VC a jami’ar ta BUK kafin daga bisani tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugabancin hukumar kula da jami’o’i 
Amma da yake jawabi a wajen liyafar da jami’ar ta shirya domin yi masa maraba, Farfesa Rasheed ya ce ya bar mukamin ne don kawai ya ci gaba da koyarwa har ya kai yin ritaya. 

Da yake jawabi, ya ce aikin da ya fi ba shi sha’awa shi ne koyarwa, don haka ya dawo jami’ar don ci gaba daga inda ya tsaya. 

PLAY ▶️

A cewarsa: “Duk tsawon rayuwata, aikin da na fi so shi ne koyarwa. Amma, abubuwa kan bijiro, abubuwa suka taso da suka min barin aikin jami'a. 

Hakazalika, ya bayyana yadda ya taba barin aikin a baya na tsawon shekaru shida, amma ya sake dawowa don ba da gudunmawarsa. 

Ya kuma bayyana cewa, bayan barin NUC, wata jami’a mai zaman kanta ta yi masa tayin biyansa albashin Naira miliyoyi duk wata idan ya amince zai yi aiki da ita, amma ya ki saboda burin zama a BUK.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa Najeriya ke ci gaba samun kafuwar jami’o’i masu zaman kansu, Farfesa Rasheed ya ce har yanzu kasar na bukatar karin cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu don cike gurbin karatu ga dalibai duk shekara. 

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba