Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Mata Da Miji Sun Yi Basaja a Matsayin Sabbin Shiga Musulunci Inda Suka Yi Wa Babban Liman Sata a Yobe

Yobe - Jami’an ‘yan sandan jihar Yobe sun cafke wasu ma’aurata, Abdullahi Ibrahim da Khadija Ali bisa zargin satar babur na wani malamin addinin musulunci a ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe. 

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu kamar yadda PM News ta wallafa. 
Kakakin ya ce Ibrahim mai shekaru 21 da Khadija mai shekaru 20, a ranar 4 ga watan Yuni sun je, wajen malamin da zummar cewa suna so su Musulunta. 

Ya ƙara da cewa sun gabatar da kansu a matsayin Jude Emmanuel, ɗan ƙabilar Birom daga Farar-Kasa a Barkin Ladin jihar Filato da matarsa, da ta bayyana sunanta da Peace Sunday. 

Kakakin ya bayyana cewa bayan musuluntar da su ne, sai aka ce su zauna wajen babban Limamin Fika domin koyar da su ilimin addini da sauran abubuwa. 

Dungus ya kuma ƙara da cewa bayan kwana ɗaya ne Abdullahi ya sanar da limamin cewa yana so ya samu toka daga wurin da tsawa ta faɗa don ya haɗa wani magani. 

A kalamansa ya ci gaba da cewa: “Liman ɗin ya haɗa shi da ɗaya daga cikin ‘ya’yansa don ya kai shi wani daji da ke kusa. Bayan isarsu wurin ne wanda ake zargin ya ɗebo ƙasar ya taho da ita.” 

“A rana ta uku mutumin ya ƙara neman a sake kai shi wurin da zummar ɗebowa matarsa ƙasar. A rannan sai limamin ya sa ɗansa ya kai shi a kan babur ɗinsa.” “Isarsu wurin ke da wuya sai suka yi wa yaron fashin babur ɗin sannan kuma suka arce da shi.” 

Dungus ya bayyana cewa a ranar 1 ga watan Yuli, 'yan sanda sun samu bayanai da ke nuni da cewa an ga ma’auratan a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno, suna shirin aikata makamancin abinda suka aikata. 
Sai dai ya ce dubunsu ta cika a ranar 5 ga watan Yuli, da misalin ƙarfe 02:00 na rana, yayin da jami’an tsaro suka yi nasarar cafke su. 

Daily Post ta ruwaito cewa Abdullahi asalinsa Musulmi ne, kuma sunansa kenan Abdullahi, ɗan garin Sabon Garin Mai Mala da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe. 

Haka nan ita ma matar ainihin sunanta kenan Khadija Ali, yar asalin jihar Gombe.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba