Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Yan Kannywood Sun Kadu Kan Mutuwar Auren Jaruman Kannywood Biyu Hafsat Idris Da Na Zahrau Shata

WASU ‘ya’yan masanaantar finafinai ta Kannywood sun bayyana damuwa kan mutuwar aurarraki biyu – na tsofaffin jarumai Hafsat Idris da Zahra’u Shata.

A ganin su, mutuwar aurarrakin za ta ƙara ƙarfafa ƙaryar da wasu ke yi cewa ‘yan fim mata ba su son zaman aure.

‘Yan Kannywood ɗin sun bayyana damuwar ne lokacin da mujallar Fim ta nemi jin abin da za su iya cewa kan ganowar da ta yi cewa auren kowacce daga cikin waɗannan matan ya mutu kuma tuni kowacen su ta daina zama da mijin ta ta kama gaban ta.

Ba yanzu ba ne aurarrakin waɗannan tsofaffin jaruman su ka mutu, domin kuwa an shafe watanni, to amma kafin wannan lokaci wasu masu lura da al’amuran industiri sun daɗe su na ɗora ayar tambaya kan yadda waɗannan matan su ka buɗe sabuwar mu’amala wadda ta bambanta da yadda su ka riƙa gudanar da rayuwar su a matsayin matan auren a baya.
Kowaccen su ta ƙara himma wajen ɗora saƙwanni a soshiyal midiya, musamman a Instagram da TikTok, sannan an gan su sun tsoma ƙafa cikin harkokin Kannywood.

Zahra’u Shata dai ta yi suna ne a fagen fim daga wajen shekarar 2000, sannan ta yi auren kece raini da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Marwan a Kano a cikin 2004. Wato kenan ta yi zaman aure na tsawon shekaru 19.

A cikin tsawon shekaru, ta riƙa wallafa hotunan ta da na ‘ya’yan a Instagram masu alamta cewa lallai ta mori miji.

Majiya mai tushe ta faɗa wa mujallar Fim cewa auren ya mutu “tun wajen Janairu na wannan shekara.”

Da auren ya mutu, sai tsohuwar jarumar, wadda jikanyar shahararren mawaƙi Alhaji Mamman Shata ce, ta zauna a gidan mijin har ta gama idda, wanda “hakan ne ma ya sa daga ita sai ‘yan’uwan ta da ƙawayen ta na kusa ne su ka san labarin.”

“Amma dai a yanzu ta tashi daga gidan, ta kama  hayar wani makeken gidan a Tudun Yola inda ta kwaso ‘ya’yan ta ta ke zaune da su,” inji majiyar.

 ‘Ya’yan su ita da Marwan guda huɗu ne – maza uku da mace ɗaya ‘yar’auta.

Wata daga cikin ƙawayen Zahra’u ta faɗa wa mujallar Fim cewa: “Duk da akwai sirri na ma’aurata a game da rabuwar aure, amma dai gaskiya Zahra’u ta taka muhimmiyar rawa wajen mutuwar auren ta, saboda ta biye wa ƙawaye da ta ke ganin su na yin rayuwar da su ka ga dama kuma su na samun kuɗi da manyan gidaje da motoci, don haka ta ke ganin kamar zaman auren ya hana ta taka wannan matsayin. Wannan ya sa ta ga rabuwar auren ya fi mata. Don haka ko da akwai wasu dalilai, shi ma wannan ya na daga ciki.”

‘Yan fim da su ka san da labarin mutuwar auren sun nuna matuƙar damuwar su ga mujallar Fim.

Wata tsohuwar jaruma da ta ke zaman aure a yanzu, wadda ta buƙaci mu sakaya sunan ta, ta faɗa wa wakilin mu cewa: “Ni wallahi lokacin da aka ce auren Zahra’u ya mutu da ƙyar na yi barci a daren, kawai na kwanta ina ta juye-juye.”

Ƙoƙarin da wakilin mu ya yi na jin ta bakin Zahra’u ya ci tura domin duk kiran da ya yi mata ta waya ba ta amsa ba, wanda a da ba haka abin ya ke ba.

Ita kuma Hafsat Idris, wadda aka fi sani da Hafsat Ɓarauniya, mun ba ku labarin sun yi aure a asirce ne da wani matashi a Kano mai suna Mukhtar Hassan Hadi, a ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022.

Wata makusanciyar jarumar ta ce lamarin mutuwar wannan auren bai mata mamaki ba “saboda aure ne da ake ganin an yi shi na sha’awa da biyan buƙata a ɓangarorin biyu.”

Majiyar mu ta ce: “Hafsat ta auri ƙaramin yaro da ta girme shi nesa ba kusa ba, kuma iyayen sa ba su son auren tun da farko. Sun so ta auri sa’ar sa kuma wacce ba ‘yar fim ba.”

Majiyar mu ta ce dalilin rabuwar su shi ne akwai “manyan bambance-bambance” a tsakanin su na yadda kowanne ya ke ganin ya kamata a yi zaman.

Wakilin mu ya samu labarin cewa auren ya mutu ne kusan watanni bakwai da su ka wuce, amma ba a gane ba domin Hafsat ta na zaune ne a gidan ta, ba gidan angon ba. Don haka ba sai an gan ta ta na famar kwashe kaya ba ko canza gida ba.

“Haka kuma ta riƙa shiga cikin dangin sa, har ana yin bukukuwa tare da ita,” inji wata majiyar.

Ta ƙara da cewa: “Amma na ji an ce Hafsat Ɓarauniya na so a maida auren, shi Mukhtar ɗin ne bai ba da haɗin kai ba.”

Tuni dai Hafsat ta dawo ruwa cikin harkar fim tsundum, inda a yanzu haka ta na daga cikin jaruman da ake ɗauka a shirin dirama mai dogon zango na furodusa Abdul Amart Mohammed, wato ‘Manyan Mata’.

Kwanan nan an gan ta a wajen ɗaukar fim ɗin a Kaduna, kuma “kai da gani ka san ba ta da aure,” inji wani ɗan wasa wanda ya halarci ɗaukar fim ɗin.

Mutuwar auren manyan jaruman Kannywood mata na baya-bayan nan ta haɗa da ta Mansurah Isah, Shamsiyya Habib, da Wasila Isma’il.

Comments

Popular posts from this blog

Ankai Sheikh Aminu Daurawa Bango Yayi Murabus Daga Kan Shugaban Hukumar Hisbah Na Jihar Kano