Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Yan Sanda Zasu Buga Wasan Kwallo da Tubabbun Yan Daba a Kano

Kano state - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Kano ta ce zata shirya wasan kwallo na musamman tsakanin jamianta da kuma tubabbun 'yan daba.
Kwamishinan yan sandan Kano, Muhammed Usaini Gumel, shi ne ya tabbatar da haka inda ya ce zasu yi wasan ne domin tabbatar da cewa yan daban sun yi tubar gaskiya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa
kwamishinan ya fadi haka ne yayin nuna mutum 108 da 'yan sanda suka kama kan zargi dban- daban lokacin shagulgulan babbar Sallah.

A kalamansa, CP Gumel ya ce:

"Zamu bi hanyoyi daban-dabn domin sauya rayuwar yan daba su zama mutanen kirki. Zamu shirya gasar kwallo, zamu taka leda mu kara da, zamu buga wasan cikin gida."

'A yanzu hankalin mu ya koma kan sabbin hanyoyin da yan daba suka bullo da su musamman a cikin kwaryar birnin Kano, ba zamu yi kasa a guiwa ba, mun tsara dabaru da fasahar shawo kan aikata manyan laifuka a sassan Kano."

Bayan haka, kwamishinan 'yan sandan ya bayyana sunayen wasu manyan 'yan dabaa sassa daban daban, kuma ya umrci su mika kansu hannun 'yan sanda tun da arziki.
PLAY ▶️

Sunayen da ya ambata sun hada da, Messi na Kan Tudun Dala; Dan Boss daga Dala Makabarta, Ado Runto a Tudun Fulani; Baffa Makashi a Mazaunar Tanko Quarters da Kamilu Duna a Adakawa Quarters.

Ya ce dukkan wadanda nan da wasu da ya bayyana sunayensu, su hanzarta mika kansu idan ba haka ba, hukumar zata ayyana nemansu ruwa a jallo.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba