Jaridar Dclhausa ta samu tattaunawa da malama Juwairiyya usman suleiman akan batun da ake tattaunawa satin da yagabata har zuwa yanzu a cikin wani shiri na talabijin arewa24tv “Mata A Yau” inda wata daga ciki tace tana mamakin yadda za’a ce dole ne sai mace ta gaida mijinta.
Wanda daya daga ciki masu shirin take cewa idan matarka bata gaisheka ba sai ka gaisheta amma bata ga dalilin saken mace dan ta rasa gaida mijinta ba da sunka kwana gado daya.
Dclhausa sun samu tattaunawa da malama Juwairiyya usman suleiman wanda malama ce ta da tafi fice wajen wayar da kan al’umma musulmi musamman mata yan uwanta ga yadda tattaunawar ta kasance.
.“wane yare ne ko wata al’ada ce tace mace bazata gaida mijin ta ba? Babu yare daya a cikin al’ada wanda munsan musulunci yana mutunta al’adun mutane, wane yare ko addini yace miji shine zai gaida mace.
Wakilin Dclhausa : ya tambayi malama Juwairiyya usman suleiman cewa da kece mijin ya kawowa karar matarsa bata gaisheshi zai sake ta me zaki ce.
Malama Juwairiyya: da nince Juwairiyya anka kawowa wannan karar da farko zan tatatausa mijin akan matarsa bata gaisheshi, saboda dole sai an saurare na kowa daga ciki domin idan ana son ayi sulhu.
Za’a tambaye shin miyasa saboda anji kawai yace zai saki matarsa saboda bata gaisheshi da safe tana jiran ya gaisheta sai tsaya ayi bincike akan miyasa hakan ta faru , idan anyi bincike shi a lurar da shi akan wannan maganar itama sai a samu mafita amma ba wai kawai a kawo wannan maganar wai shi miyasa bazai gaisheta wannan ba magana mai daɗi bace.
Mai tambaya: akwai masu ra’ayin cewa shin ya kamata a daidai cewa idan yau mace ta gaida mijinta gobe mijin ya gaida matarsa shin ko akwai ayoyi ko hadisi da yace dole ne sai mace ta fara gaida mijinta.?
Malama Juwairiyya: na fada na sake fada a gidan Annabi s.a.w shi yake bin matansa yana gaishe su , so idan kayi haka ba laifi kayi ba, amma ke matar ya zakiyi ki karbi wannan , mata yanzu suna da gadara muna maganar ‘yanci nan da muke fada waye ne ya bamu yancin fiye da musulunci akwai inda anka samu yanci fiye da musulunci babuta”.
Duba da irin idan munka ce sai mun rubuce duk maganar akwai bayyani sosai amma zamu ta ƙaita a nan sai ku saurari cikakken bayyanin a cikin faifan bidiyo.
Comments
Post a Comment