Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Shahararren ɗan Wasan Kwallon Kafar Ahmad Musa Ya Taimaki Baba Karkuzu Da Makudan Kudi

Shahararren ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya, Captin Ahmed Musa MON ya ba da umarnin a Nemo gida wanda kuɗinsa ya kai Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zai sayawa ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu, sannan kuma a yanzu haka ya aike masa da tallafin kuɗi Naira 500,000 domin ya yi cafane duba da halin ƙunci, matsi, gami tsananin rayuwa da ya ke ciki.

Cikin wata tattaunawa da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da shi, Captin Ahmed Musa ya bayyana cewa “Na yi magana da Baba Karkuzu ta waya, na kuma tabbatar masa na ba shi tallafin Naira 500,000 ya yi cafane. Bayan haka kuma na shaida masa cewa na ba da umarnin a nemo masa gida na Naira Miliyan 4 zuwa Naira Miliyan 5 zan saya masa daga nan kuma mu ga tayadda zan ƙara taimaka masa”. In ji Ahmed Musa.
A ƴan kwanakin nan ne dai aka jiyo tsohon ɗan wasan Hausan, Baba Karkuzu ya na kokawa kan halin ƙunci da ya ke ciki, tayadda har ta kai ya makance ba ya iya gani saboda ƙuncin rayuwa, har ma wasu ke nema masa tallafi a Social Media domin a taimaka masa.

“Sama da shekaru 43 Ina harkar Fim, amma yanzu sai a wayi gari babu abinda za a ci a gidana. Kuma yanzu haka na daina gani, sannan kuma gidan da na ke ciki mai shi ya saka shi a kasuwa”, Cewar ɗan Fim ɗin Hausa, Baba Karkuzu.

Wannan labarin ya taɓa Captin Ahmed Musa sosai ya yi jimamin halin da Baba Karkuzun ya ke ciki, domin tun ya na yaro a birnin Jos ya ke ganin wasannin Baba Karkuzun a gidan talabijin na NTA. Ganin haka ya sa Captin Ahmed Musa ya nema ya yi magana da shi ta waya ya kuma yi masa wannan albishir da wannan tallafi na gida da kuɗi.

Captin Ahmed Musa mutum ne wanda ya yi shuhura wajen taimako da jinƙan al’umma, ko da a baya-bayan nan, ya sayawa wasu matasa mutum 4 manya-manyan gidaje a Kano domin su zauna da iyalansu.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba