Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Wata Tsaleliyar Budurwa Tayi Bayani Kan Dalilin Dayasa Take Shan Shaka Fasha Domin Samari Su Ga Tayi Kyau

Al’adar shan magunguna dai don kara ƙiba na ci gaba da zama ruwan dare a ƙasarnan musamman arewacinta duk da irin gargadi da likitoci ke yi kan illar hakan.jaridar dimokuraɗiyyar ce ta ruwaito wannan labarin

Toh amma duk da haka yan mata da matan aure sun dauki hakan tamkar wani ado ne don burge jama’a.

Wakilinmu a Bauchi Bashir Khalid Furyam ya tambayi wani ƙwararren likita game da illar hakan, inda ya tabbatar da cewa maganin na sha-ka-fashe na da matukar illa musamman yayin haihuwa.
Dakta Hassan Garba wanda likita ne a asibitin Palycon dake cikin garin Bauchi ya tabbatar da cewa magungunar na sha -ka-fashe na haifar da cututtuka kamar su hawan Jini da cutar daji da ciwon Shuga da kuma ciwon zuciya sakamakon irin karfin sinadaran dake cikinsa.

“Wannan magani ya fi illa wa mata, saboda garkuwar jikinsu ba ta kai ta maza ƙwari ba, hakan ya sa da zarar sun yi amfani da magungunan sai ka ga ya fara tasiri a kansu”.

Toh sai dai duk da irin wadannan gargaɗi da likitoci irin su Dakta Hassan Garba ke yi, mata da dama na ci gaba da tsunduma gadan-gadan cikin wannan dabi’a kamar yadda wata matashiya a Bauchi ta shaida wa wakilin namu.

Matashiyar wacce ta buƙaci a sakaye sunanta, ta ce tana shan magungunar ƙara ƙiba ne sakamakon irin yadda samari ke nuna sha’awarsu ta son mace mai ƙiba da kuma irin yadda ake wa mata gori a guraben bukukuwa

“Gaskiya dalilin da ya sa nake shan sha-ka-fashe shine irin yadda na ga yanzu kowa da kowa musamman samari, sun fi so su ga mace a cike kamar za ta tumbatsa, toh ni ma kuma ba na so a yi banda ni”

Toh sai dai duk da kasancewar matashiyar ta ce ba ta fara fuskantar wani kalubale ba sakamakon magungunar, amma ta ce tana fatan dainawa don gudun abinda zai kai ya komo.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba