A shekaranjiya ne anka wani gari da ganin hoton fitacciyar jaruma yar Tiktok murja Ibrahim kunya an mata duka har da rauni sosai jini a fuskantar ta
Abun ya baiwa mutane mamaki wannan wane irin mutane ne sunkayi murja kunya wannan rashin daraja, abun ya baiwa mutane mamaki kowa yana so yaji dalilin yi mata wannan aika-aikar,To yanzu majiyarmu ta samu wani faifan bidiyo wanda wata jarumar tiktok Hafsat waziri wadda anka fi sani da babiana ta bayyana Dalili dalla dalla .
Babiana Ta Fara Da Ccewa 'Innalillahi wa’innah alaihi Raju’un to abin naka in na shiriya ne Allah ya shiryeka idan kuma abin naka bana shiriya bane Allah ya tsine maka albarka tunda haka kaso, yanzu fisabilillahi ina kai ina murja, nayi muku iyaka kai da ita ka fita sabgarta tunda tace bata iya sana’ar sayar da fata da gantaba, shine abin bai isheka ba sai da ka tura yan iska ankayi mata naushin munana suka fisge mata gira kwaya daya.
Ta Kara Da Cewar 'Ni wallahi kiran sunanka ba abu ne da nake tsoro ba, wallahi idan banzo na tuna maka asiriba
Babiana ta kara da cewa mu yan Masana’atar titkok zamu bayyana sunanka muyi maka tirere bazamu lamunci haka ba. Abu ukku muke so mukawo a cikin titkok din nan,Mukawo “sanity” tsafta kenan,Mu rika kwatowa mata ‘yancin su da maza,mu rika zama da mutane murinka jin matsalolinsu muna biya musu,Bazai yiyu a taba dan midiyarmu ace kada muyi magana ba, sai munyi magana koda kashe mu za’a yi.
Daga Karshe Babiana tayi kira ga ilahirin jama’ar titkok da su fito Suje Su kwatowa murja ‘yancinta To Allah Ya Kyauta Anan Kuma Wani matashine mai suna Abubakar Nasir Barda, yana aji 2 a jami’ar gwamnatin tarayya ta FUDMA da ke garin Dutsinma a jihar Katsina Ya Mutu Ake Zargin Abokansa Ne Dalibai Suka Kashe Shi
Ana zargin wasu ɗalibai Inyàmúrái àbokan karatunsa sun kàshé shi ta hanyar yi màshi bugun tàron dangi sakamakon takun saƙar da ya shiga tsakaninsu akan rikicin soyayyar wata ɗaliba mai suna Joy wacce ya samu gurbi a zuciyarta, inda suka yi ta búgunsà da itatuwa sai da ya mutu har lahira.
A bayanan da muka samu ɗaliban da ake zargi da kisan Abubakar, sun fasa masa kai saboda tsananin duka inda jini ya riƙa fita ta hanci ta baki har sai da ya faɗi ƙasa wanda daga bi sani aka kai shi asibitin makarantar, amma daga ƙarshe Allah ya karɓi ran shi.
Abubakar ya gamu da àjalinsa ne, a daidai lokacin da ya ke zana jarabawar ƙarshe ta aji biyu a jami’ar,Wannan babban abin takaici ne da Allah wadai ga ɗaliban da suka yi wannan aika aikar ga Abubakar, wanda ya kamata ayi gaggawar bi mashi haƙƙinsa
Dan Gwagwarmaya Comr Nura Siniyo Ne Ya Wallafa Wannan Labarin Inda Daga Karshe Yake kira ga mahukunta da su gaggauta ɗaukar matakin hukunci ga waɗannan azzaluman ɗaliban mara sa imani da tausayi da suka yi mashi wannan aika aikar tare da biyan iyalansa diyya Muna Addu’ar Allah ya jiƙanshi da rahama ya gafarta masa yasa Aljannan ce makomarsa.
Comments
Post a Comment