Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Subhanillahi Matsin Na Nijeriya Zata Shiga A Nan Gaba Sai Ya Fi Na Yanzu

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya ce gwamnatin da ta gabata ce ta jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arzikin da take ciki a yanzu.

Muhammadu Sanusi na II, wanda ya jagoranci Babban Bankin Nijeriya daga 2009 zuwa 2014, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da laifi kan halin da ake ciki a halin yanzu domin kuwa ta gaji matsalolin da ake ciki ne. Jaridar TRTAFRIKA na ruwaito wannan rahoto

Ya bayyana haka ne a wani sakon bidiyo da aka watsa a shafin Instagram a karshen mako.

Ya kara da cewa ya dade yana gargadi kan a gyara matsalolin da ya hango wa kasar amma aka ki gyarawa.

Tsohon shugaban Babban Bankin Nijeriya ya ce duk wanda ya ce gwamnatin Tinubu ce ta jefa kasar cikin matsin da ake ciki a yanzu “ya zalunce ta” saboda ba laifinta ba ne.
Ya ce mutane na ta rubuto masa wasika cewa ana yunwa a kasa amma ya yi gum da bakinsa.

“Ana yunwa, ya kamata a ce mun yi magana amma ba mu yi magana ba, to ni me zan ce? Shekara nawa na yi ina gaya wa mutane cewa wannan wahalar na gabanmu?” in ji Muhammadu Sanusi II.


Ya ce tun lokacin da ya ga an dauki hanyar da ba ta dace ba wurin tafiyar da tattalin arzikin Nijeriya ya san cewa a karshe wahala za a sha.

“Wahalar da ake ciki a yanzu, ta gaba ma ta fi ta,” a cewarsa yana mai karawa da cewa akwai kasashen da a baya suka fuskanci makamancin abin da ke faruwa a Nijeriya.

“Kafin a yi zabe an yi taro a Kaduna, lokacin shi Tinubu yana zaune, na fada na ce duk wani dan siyasa da ya ce muku ba za a sha wahala ba, kada ku zabe shi.

“Su masu cewa na yi magana a yanzu, lokacin da nake magana a kai me suka ce mini? Ce wa aka yi siyasa muke yi, ba ma son gwamnati, muna sukar shugaban kasa,” in ji tsohon gwamnan Babban Bankin na Nijeriya.

Khalifan na Tijjaniya ya ce an shafe shekara takwas ana rayuwa ta karya a Nijeriya inda ya ce an ci ba shi a kasashen waje da cikin gida haka kuma babban bankin kasar ya bayar da bashi na cikin gida kusan naira tiriliyan 30.

“A gwamnatin da ta gabata, sai da ta kai dukkanin nairar da gwamnatin tarayya take samu ba ta biyan kudin ruwa a kan bashi.

Comments

Popular posts from this blog

Ankai Sheikh Aminu Daurawa Bango Yayi Murabus Daga Kan Shugaban Hukumar Hisbah Na Jihar Kano