Daga Ahmad Nagudu
Duk da ina ganin sunan yarinyar nan Rahama kuma Sa'idu, wallahi ban taba zato ko daukar a musulma ba a iya sanin da na yi mata.
Domin kwatakwata tsarin rayuwar ta bai yĆ karma da na yayan Musulmai masu mutunci ba. Kamar yadda na fada a baya, wallahi ko ni ne ki ke makarantar da na ke Shugabanci, sai na sallame ki.
Domin a hankali za ki kwadaitawa wasu masu raunin zuciyar irin kazarmar rayuwar da ki ke dabbakawa. Kurma ko da ki na makarantar ma, ni ban yadda ki na zama a cikin ta kamar sauran Daliban kirki ba.
Domin kullum ke ce Abuja, Kaduna, Kano, Lagos, me ki ke zuwa yi can? Ki na da yan uwa ko dangi a can ne? ldan ma kina da su, da yawan Videos na ki, a dakunan Hotels ki ke yin su a garuruwa daban-daban.
Ki na mace, yarinya karama haka, wannan halin kirki ko tarbiyya ne? Babu Wadda za ki yaudara da wannan kukan munafunci da rainin wayon na ki! You're doing all these just to call people attentions on you.
While, ba ki fito kin gayawa duniya ke na ki laifin ba. Ki na Musulma, amma kulum kai babu dankwali, ki na ta gantali da jiki a bude, sannan ki na zaton za a zuba ido a bar ki, ki ci gaba da yi ko? To, idan iyayen ki sun kasa kula da ke da tarbiyyar ki, da sa ido akan abubuwan da ki ke yi, ita Hukumar makaranta, ba za ta saka ido ba.
Domin ba iya karatu kadai ake koya a makaranta ba, har da tarbiyya. Wannan kuma shine hukuncin da ya dace da ke kawai.
Sannan tun da kin ce kina business, wanne business ki ke yi alhalin dalibar makaranta ki ke? To, idan ma har hakan ne, ki je ki cigaba da business din ki mana kawai, tun da shine abun da ki ke rufawa kan ki asiri da iyaye da kannen nan ki. Kamar shine da abun da ya fi dacewa da ke ba karatun ba.
Domin dama ai da irin wannan raye-rayen ki ke samun kwastoma ai ko? Shi kuma karatun ai dama ba kudi ake baki ba, to meye na damuwa.
Yar rainin hankali kawai. To, daga karshe ma dai, ga nan Hukumar Makarantar ta fito ta bayyana gaskiyar lamarin abun da ke faruwa. Wadda dama sai da na yi wannnan tunanin a cikin rubutun nan a sama.
Babu ta yadda za ka bibiyi shafukan ta, ka ga irin rayuwar da ta daukarwa kan ta, ta ke yi, sannan a ce za ta mayar da hankali a kan karatu ko neman ilmi.
Zai yi matukar wahala wannan kam wallahi. Don layin ba ma daya ba ne.
Bayyanar da tsiraici, bibiyar wakokin mawaka a mabambantan wurare, shigar banza da sauran Su. Kuma duka bidiyoyin da ta ke yi, babu wadda za ka gan ta da shigar mutunci ko a makaranta da ke nuna alamar karatu ko ta ke yi. Wadda wannan ke nuna ba shi da wani muhimmanci a gare ta.
Jama'a, an kori wannan yarinyar daga makaranta ne sakamakon faduwa jarrabawa da ta yi, kuma ba ta zo ta gyara ba.
Daga nan sai da ta shafe kusan wata 5 ba ta shiga Aji da sunan karatu alhalin ta na matsayin dalibar makarantar, wannan ya sa Hukumar Makarantar su ka rubuta takardar kora su ka aika mata.
Amma da ya ke gogaggiya ce a bariki, shine ta ke neman wawantar da tunanin mutane ta hanyar murde ainahin yadda gaskiyar lamarin ya ke, ta fitar da wani labarin karya don ta jawo hankalin mutane zuwa kan ta.
Comments
Post a Comment