Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Hukunchi Yin Tazarar Haihuwa A Musulunchi Family Planning

π“π€πŒππ€π˜π€❓

Shin ko akwai dalilai na shariah da suke halatta mace ta juyar da mahaifarta ko kuma ta samu tazarar haihuwa?

π€πŒπ’π€❗️

 To Ι—an'uwa amfani da abin da zai kayyade iyali, ya kasu kashi biyu:

1. Ya zama zai hana Ι—aukar cikin kwata-kwata, a nan bai halatta ba, saboda ya saΙ“awa manufar shari'a na yawaita al’uma, kuma ‘ya’yan da take da su za su iya mutuwa sai ta koma mai wabi.

2. ya zama an tsayar da shi ne na dan wani lokaci, kamar mace ta zama tana yawan haihuwa kuma cikin yana wahalar da ita, sai ta yi nufin ta tsara haihuwarta ta yadda za ta haihu duk bayan shekara biyu ko makamancin haka, to wannan ya halatta in dai miji ya bada izini kuma ba zai cutar da matar ba, dalili akan haka shi ne sahabbai sun kasance suna AZALU a zamanin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam don kar matansu su Ι—auki ciki, kuma ba’a hana su ba, kamar yadda Bukari ya rawaito daga hadisin Jabir mai lamba ta: 4911.
.
Abin da ake nufi da AZALU shi ne idan namiji yana saduwa da matarsa idan ya ji maniyyi zai fito sai ya fitar da azzakarinsa ya zubar da maniyyin a wajen farji.

Duba Dima'uddabi'iyya na Ibnu Uthaimin shafi na 57.

Sannan kuma an haramta:

*VASECTOMY* wato kashewa 'ya'yan maniyyin namiji. Idan akayi ma namiji irin wannan aikin, to zai iya yin Jima'i amma har abada ba zai haihu ba.

*TUBECTOMY* shima haramun ne. (Daurewa bakin mahaifar mace, ta yadda Qoyin halitta ba zai samu damar shiga ba). Idan aka yiwa mace irin wannan aikin, to har abada ba zata sake haihuwa ba. Domin kuwa Qwan halitta ba zai samu damar shiga ba, ballantana har maniyyi yayi fertilizing Ι—insa.


Ba'ayi sai dai idan matar ta kasance anyi mata operation sau da dama, kuma likitoci sun bada tabbacin cewar ba zata iya rayuwa ba idan aka sake yi mata wani operation Ι—in.
Hakanan irin allurar da ake yiwa mata domin kashewa Qoyin halittar Ι—an adam (gaba Ι—aya) daga cikin mahaifarsu. Itama haramun ce.


Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba