Jarumin masana'antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya nesanta kansa daga rade-radin da ake yi na cewar shi dan daba ne a baya Sadiq wanda aka fi sani da Gambo uban Tani ya ce shi dai ya yi farauta a lokacin da yake tasowa
Jarumin fim din ya ce duk da rashin jin da ya yi, Allah bai kaddare shi da yin shaye-shaye ba Shahararren jarumin masana'antar shirya fina- finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya karyata rade-radin cewa shi dan daba ne a baya.
Da yake amsa tambayoyi a shirin "Gabon's Room Talk Show' wanda jaruma Hadiza Aliyu Gabon ke gabatarwa a Youtube, jarumin ya ce shi mafaruci ne a lokacin da yake tasowa.
Ya ce shakka babu ya dan taba rashin ji da yake tasowa domin har ya yi sana'ar siyar da mai na bunburutu.
Sai dai ya ce duk da kasancewarsa dan
bunburutu bai taba yin shaye-shaye ba amma dai fada ko dambe bata yi masa wahala a lokacin.
"Mutane ne basa bambancewa, akwai dan daba, akwai mafarauci. Ni mafarauci ne, na yi farauta a lokacin da nake ganiyar kuruciya da kuma rashin. Na yi farauta, na dan taba farauta gefe-gefe haka sannan kuma na siyar da mai irin na jarka- jarka black market kuma yawancin wanda ya yi wannan sana'ar za a gan shi ba shi da tsoro.
Toh ni ba dan daba bane amma ni mafarauci ne ko yanzu dama ta samu idan na samu nutsuwa ta wani gefen na kan yi harbi in fasa in yi ciki.
"Rashin ji da na yi a harkar farauta da na yi, kin san akasari a cikin kashi dari, kashi tamain na mafarauta suna da fushi saboda wasu dan abubuwa da ake amfani da su, za ka ji kai kadai kana zaune musamman idan aka dan kada wani gangan za ki ji ka soma tsuma.
"Abun fada baya yi mun wuya a da, yanzun nan sai in tube riga mu daku da ke ba damuwa bane. Sai ni ban yi shaye-shaye ba inda Allah ya taimake ni kenan, duk rashin jin da na yi Allah bai kaddaramun shaye-shaye ba, shima kuma saboda addu'an iyaye ne."
"Ina Sa Rai Sanadiyar Kannywood Zan
Samu Gidan Aljannah", Inji Sadiq Sani Sadiq
A baya, mun ji cewa jarumin fim Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da 'Garmbo uban Tani, ya bayyana cewa yana fatan firn ta zama silar shigarsa gidan Aljanna.
Sadiq ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a shirin abokinyar sana'arsa jaruma Hadiza Aliyu Gabon mai taken 'Gabon's Room Talk Show' wanda take gabatarwa a shafin Youtube.
Comments
Post a Comment