Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Kotu Ta Yankewa Ƴan Daudu Hukuncin Wata 3 a Gidan Gyara Halinka da Bulala 10

Kotun Shari’ar Addinin Musulinci dake zaman ta a Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta yankewa, wasu yan Daudu Hukunci, bayan sun yi shigar mata dan yin rawar karya kwankwaso a wajen bikin uban gidansu, mujallar hisah kano na wallafa a shafin na sada zumunta.

Kotun Karkashin Jagorancin Mai Shari’a Mallam Sani Tamim Sani Hausawa, ta samu matasan yan Daudun da laifin bayan an karanto musu kunshin tuhumar da ake yi musu, inda nan ta ke suka amsa , sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.
Mai shari’ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar naira dubu goma-goma kowannen su, tare da yi musu Bulala goma-goma.

Mukaddashin Kwamandan Hukumar Hisbah na Jahar Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar , ya bayyana cewa hukumar ba zata gajiya ba , wajen dakile aiyukan Badala , domin aikin hukumar shi ne ,yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.

Comments

Popular posts from this blog

Ankai Sheikh Aminu Daurawa Bango Yayi Murabus Daga Kan Shugaban Hukumar Hisbah Na Jihar Kano