Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Kai Tsaye Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Shari'ar Abba Gida Gida Da Gawuna Ka Kujerar Gwamnan Kano

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al'ada
Abuja - A safiyar Juma'a, kotun daukaka kara mai zama a birnin tarayya watau Abuja za ta yanke hukunci a shar'ar zaben Gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya samu kuri'u 1,019,602 a zaben da aka yi, Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya zo na biyu ya samu kuri'a 890,705.

Da APC ta je kotun daukaka kara, Alkalai sun rage fiye da 165, 000 daga cikin kuri'un NNPP saboda rashin sa hannu da hatimi, aka ba APC nasara.

Shari'ar nan ne Abba Kabir Yusuf ya kalubalanta a wannan kotu, APC kuma ta roki a tabbatar da hukuncin da karamar kotun zaben ta zartar a Satumba.

Kotu ta tsige Abba Kabir Yusuf Bayan sauraron shari'ar, Alkalan kotun daukaka kara sun tsige Abba Kabir Yusuf bisa dalilali da hujjojin jamiyyar APC.

Hukuncin Kano ta Zoom Kotun ta zartar da cewa yin hukunci ta Zoom a maimakon a zauna a harabar kotu ba laifi ba ne, an yi watsi da korafin Wole Olanipekun
Nasiru Gawuna ya kubuta?

Barista Hikima wanda yake kawo bayanai daga kotun ya rubuta a shafinsa cewa kotu ta ce: "Ba dole bane sai APC ta saka sunan Nasir Gawuna wajen shigar da kara ba."

P1730: Kotun karar zabe ta yi daidai
Kotun daukaka kara ta ce karamar kotu ba ta saba doka da ta karbi takardun da lauyoyin jam'iyyar NNPP su ke adawa da su ba.

Kotu ta fara karanto hukunci Majiya daga kotun daukaka karan ta ce Alkalai sun fara karanto hukunci, an soma yin shimfidar korafin lauyoyin Gwamnan Kano.

An fara shirin karanto kara
Kamar yadda Barista Hikima ya fada a shafinsa, hukunci hudu za a yanke a zaman yau; uku daga NNPP sai kuma guda daga APC.

Jamian tsaro a kotu
Abba Hikima wanda shahararren matashin lauya ne a Kano, ya fada a Facebook cewa an baza jami'an tsaro kafin a fara shar'ar.

A Kano ma an dauki matakai masu tsauri domin gudun rikicin siyasa ya barke.

Kotu ta zauna
lbrahim Arif Garba wani lauya ne wanda yana kotun domin jin shariar zaben Gwamnan na Kano, ya shaida cewa an fara zama.

Kamar yadda sanarwa ta zo, zuwa karfe 10:00 ko kimanin haka za a fara hukunci.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba