Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Mace Da Ta Fara Fashi A Cikin Jirgin Sama Da Abubuwan Van Mamaki Game Da Rayuwar Ta

Mace Da Ta Fara Fashi A Cikin Jirgin Sama Da Abubuwan Van Mamaki Game Da Rayuwar Ta

Leila Khaled

Leila Khaled ita ce mace ta farko da aka sani da ta jagoranci fashin jirgin sama. Hotonta a lokacin tana budurwa, tana murmushi rike da AK-47, ya zama alama ce ta gwagwarmayar ‘neman yantar da Falasdinawa. 

An haife ta a Haifa a shekara ta 1944, ta zama ‘yar gudun hijira a lokacin korar Falasdinawa daga Nakba, wanda ake yi wa lakabi da ‘masifar, 1948, wanda ya yi sanadin korar ‘yan gudun hijira kimanin 750,000 tare da lalata daruruwan kauyuka da garuruwa tare da kafuwar kasar Isra’ila. 

Leila Khaled ta sake ganin mahaifarta Haifa sau É—aya kawai a rayuwarta - a cikin 1969, lokacin da, a matsayinta na mamba na Jam'iyyar Popular F*ront for the Libera*tion of Pale*stine, ta yi garkuwa da jirgin sama kuma ta gaya wa matukin jirgin ya tashi ta saman garinsu.

Leila Khaled ta kasance shugabar kungiyar Popu*lar Fron*t for the Libe*ration of Pales*tine (PF*LP) da ta dade tana aiki kuma ta shahara saboda da rawar da ta taka wajen sace wasu jiragen saman farar hula guda biyu, TWA Flight 840 a shekarar 1969 (wanda ke kan hanyar Tel Aviv daga Roma) da El. Al flight 219 a 1970 (mai tafiya daga Amsterdam zuwa birnin New York).

A cikin 1997, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana PF*LP a matsayin kungiyar ta'addanci, wadda ta bayyana cewa kungiyar ta kai manyan hare-hare na kasa da kasa a shekarun 1960 da 1970, ciki har da sace-sacen jiragen sama da ya kashe 'yan kasar Amurka sama da 20 . P*F*L*P kuma ita ce ke da alhakin kai hare-haren ta'ad*danci da yawa kan fararen hula Isra'ila a Isra'ila da Yammacin Kogin Jordan, ciki har da harin bam da ya kashe Rina Shnerb ' yar Isra'ila 'yar shekara 17 a shekarar 2019 da kuma harin harbe-harbe da dama wanda ya lakume rayukan masu ibada hudu a Jerusalem synagogue a cikin 2014.  

Anyi fim dinta mai suna (Leila Khaled: Hijacker) a shekarar 2016.

Leila Khaled Khaled ta shafe wani lokaci tana koyarwa a Kuwait , kuma a cikin tarihin rayuwarta, ta ba da labarin tayi kuka a ranar da ta ji an kashe Shugaban Kasar Amurka John F. Kennedy.
Har yanzu tana nan a raye da shekaru (79).

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba