Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Soyayyar Rukayya Dawayya Da Afkallahu/Matsayin Auren Aisha Aliyu Tsamiya

A Shekarar Nan Akayi Auren Tsohuwar Jarumar Kannywood Rukayya Dawayya Da Tsohon Shugaban Hukumar Tace Fina Finai Na Jihar Kano Ismael Abba Na Afkallahu Inda Yau Muka Samu Bidiyan Cikin Alfahari Jarumar Ta Wallafa A Shafin Yayin Da Suke Cikin Nishadi




Muna Musu Fatan Zaman Lafiya Da Samun Zuri'a Dayyaba Anan Kuma Satinnan Muka Kawo Muku Labarin Mutuwar Auren Jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya Kamar Yadda Muma Muka Sami Labarin Daga Gidan Jaridar Fimmagazine

Saide Bayan Dogon Bincike Da Fimmagazine Sukayi Sun Tabbatar Da Labarin Mutuwar Aure A Matsayin Labarin Kanzon Kureje Da Suka Samu Daga Majiya Marar Tushe

Mujallar Fim Sun Wallafa Cewar LABARIN da mujallar Fim ta buga jiya cewar auren tsohuwar jarumar Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya ya mutu ba gaskiya ba ne, inji ‘yan masana’antar finafinan irin su Ali Nuhu da Abdul Amart Mohammed.

Haƙiƙicewar da su ka yi tare da zurfafa bincike da mujallar ta yi ya sa mujallar ta goge labarin daga gidan yanar ta da kuma soshiyal midiya.

Jim kaɗan bayan ɓullar labarin, makusantan tsohuwar jarumar, wadda ta yi aure a Fabrairu 2023, su ka kira wakilan mu a lokuta daban-daban, su na cewa wannan labarin fa kuskure ne domin kuwa A’isha na zaune daram daƙam a gidan mijin ta.

Waɗanda su ka kira mujallar sun haɗa da Ali Nuhu, Abdul Amart, da Samira Saje,Dukkan su sun nuna cewa su na da kusanci tare da kyakkyawar alaƙa da Aisha da mijin ta mai suna Alhaji Buba Abubakar, kuma ba su daɗe da yin waya da su ba.

Samira, wadda ke da kamfanin sayar da tufafi na Samsaj Parlour da ke Abuja, ta ce ita a nata ɓangaren A’isha Tsamiya ɗin ce ma ta tura mata da labarin da aka buga tare da bayyana damuwa. Ita kuma ta yi mata alƙawarin za ta tuntuɓi masu mujallar.

Wasu daga cikin ‘yan fim ma da su ka kira labarin da “ƙarya” kai-tsaye sun haɗa da Halima Atete, Saratu Abubakar, Masa’uda ‘Yar’agadas da Sulaiman Costume.

Mujallar Fim ta bi dukkan ƙa’idojin aikin jarida wajen tattara bayanai kafin ta rubuta labarin, inda ta samu tabbacin sakin auren daga wasu mutum huɗu, ciki har da ‘yan Kannywood masu sahihin kusanci da A’isha.


Haka kuma wani wakilin mu ya yi ƙoƙarin tuntuɓar ta ta hanyar kiran waya da tura mata saƙon tes, amma babu amsa domin, kamar yadda mu ka ji a jiya, ashe ta tafi Umrah ita da wani ƙanen ta.

Mujallar Fim ta na bada haƙuri ga ma’auratan saboda rashin jin daɗin da labarin ya jawo masu, tare da tabbacin hakan ba zai ƙara faruwa ba.

Mu na yi masu addu’ar Allah ya sa mutu-ka-raba,An kafa mujallar Fim a farkon shekarar 1999, inda ta zama babbar kafar yaɗa ingantattun labarai da bayanai a kan ‘yan fim, kuma ta taimaka sosai wajen fito da da yawan su a idon duniya.

Ta shafe shekaru ashirin ana buga ta a kan takarda kafin ta bi zamani wajen ci gaba da fitowa a intanet,A tsawon wannan lokaci ba a san ta da yin ƙage ko yaɗa labarin ƙanzon kurege ba domin masu buga ta ƙwararru ne a fagen aikin jarida a Nijeriya, masu bin diddigi ƙwarai kafin su buga labari irin wannan.

Wannan Shine Abun Mujallar Fim Suka Wallafa Da Fatan Allah Ya Basu Zaman Lafiya Ameen.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba