Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu, wacce aka fi sani da Hadiza Gabon, ta maka wani ma'aikacin gwamnati mai suna Bala Musa a gaban kotun majistare da ke zama a hanyar Daura, jihar Kaduna.
Gabon ta yi karar Musa ne a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba kan zargin bata mata suna, Jarumar wacce ta magantu ta bakin lauyanta, Mista Mubarak Sani, ta ce ta sha suka da kalamai marasa dadi daga jama'a saboda kagen da wanda ake kara ya yi mata.
Ya kara da cewar mutane, musamman a soshiyal midiya sun kira Gabon da macuciya wacce ta ki auren Musa bayan ta gama karbe masa yan kudadensa wanda ta bayyana a matsayin karya Saide Wanda ake karar ta bakin lauyansa, Mista Naira Murtala, ya karyata zargin da ake yi masa.
Alkalin kotun, Shamsudeen Sulaiman, ya tambayi lauyan mai kara kan ko suna da shaidu inda suka amsa cike da tabbaci, Alkalin ya bayar da belin wanda ake zargin bisa sharadin cewa zai gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa wadanda za su zama mazauna jihar Kaduna kuma dole su zama ma'aikatan gwamnati.
Ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba domin masu karar su gabatar da shaidunsu,Saide Tun da farko wanda ake karan ya shigar da karar jarumar a kotun shari'a mai lamba 1, Magajin Gari a watan Maris din 2022. Ya zargi jarumar da kin aurensa bayan ya bata kudi N396,000.
Jarumar ta karyata batun sani Musa, cewa bata taba haduwa ko yin magana da shi ba a baya sannan babu wata alaka tsakaninta da shi.
Lauyan wanda ya shigar da karar ya gabatar wa kotun takardar banki cewa wasu mutane hudu ne suka karbi kudin da aka ce an aika wa wacce ake kara.
Biyu daga cikin mutane hudun Fatima Abdullahi da Abdullahi Yusuf, sun yi ikirarin cewa su aminiyar wacce ake kara da hadiminta ne,Sun ansa laifinsu na yi wa jarumar sojan gona tare da karbar kudi da sunan ta, inda suka rokikotu ta gafarta musu.
Bayan rokon da Murtala ya yi na mika shari'ar zuwa kotun sharĂ¯a ta gaba, alkalin wancan lokacin, Isiyaku Abdulrahman, ya kori karar sannan ya sallami Gabon a ranar 31 ga watan
Oktoba.
Da Karshe Ya umarci lauyan mai kara da wanda yake karewa da su biya jarumar N500,000 saboda bata mata lokacinta Inda Ita Kuma A Jiya Daya Ga Watan nowambar ta maka Wadda Yayi karar tata bisa Zargin Bata Mata suna a sohiyal Midiya Inda Kotu Ta dage sauraran karar Tare Da Bada belin Wadda Ake karar da Sunan Zai gabatar da shaidu Biyu A Zama Na Gaba To Allah Ya Kiyaye.
Comments
Post a Comment