Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Abunda Kotun Ki Ta Bayyana Game Da Shari'ar Gwamna Jihar Kano Abba Gida Gida Da Gawuna

Kotun Kolin Nijeriya ta ce ranar Juma’ar nan za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Jihar Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta aika wa bangarorin biyu ranar Laraba da maraice.

Lauyoyin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna sun tabbatar da cewa Kotun Kolin ta shaida musu cewa za ta yanke hukunci a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairun 2024.

Bayanai sun ce Kotun Kolin za ta bari lauyoyi biyu daga kowane bangare su halarci zaman yanke hukuncin.

A watan Nuwamba da ya gabata ne gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya garzaya Kotun Kolin Nijeriya bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da soke zabensa a matsayin gwamna.
Ya dauki matakin ne bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Kano cewa Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC ne halastaccen gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris na 2023.

A wancan hukuncin, Kotun ta cire kuri’a 165,663 daga kuri’un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri’un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

Sai dai jim kadan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a Kotun Daukaka Kara da ke Abuja yana kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.

Amma a hukuncinta, Kotun ta ce Abba Kabir Yusuf ba mamba ba ne na jam’iyyar NNPP a lokacin da aka gudanar da zaben 2023.

Wannan shari’a ta jawo ce-ce-ku-ce a Nijeriya musamman bayan da Kotun Daukaka Kara ta fitar da wasu takardu da wasu ke ganin sun ci karo da hukuncin da ta yanke. Ko da yake daga bisani Rajistara na Kotun ya ce hukuncinsu a bayyane yake.

Comments

Popular posts from this blog

Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Wasu sirrikan mata guda 10 daya kamata ku sani wanda ba kowane namiji ne ya sansu ba