Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

Kotun Ƙolin Ta Tabbatar Da Abba Kabir Yusuf A Matsayin Gwamna Jihar Kano

Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamnan jihar Kano na shekara ta 2023.

Mai shari'a John Okoro wanda ya karanta hukuncin ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar, wadda ta ce Abba Kabir bai samu rinjayen ƙuri'u a zaɓen ba.

Saboda haka nan kotun ta yi kuskure wajen zabtare wa Abba da NNPP ƙuri'u.

A game da batun rashin kasancewar Abba Kabir ɗan jam'iyyar NNPP, kotun ta ce jam'iyya ce kawai take da ikon tantance wanda ɗanta ne ko kuma a'a.Saboda haka ne kotun ta amince da ɗaukaka ƙarar jam'iyyar NNPP tare da yin watsi da hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da kuma ta sauraron ƙorafin zaɓen jihar.

Wannan shi ne mataki na ƙarshe a turka-turkar da aka kwashe watanni ana yi game da sahihancin sakamakon zaɓen na gwamnan jihar Kano.

Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri'a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam'iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri'a 1,019, 602.

Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta bai wa jam'iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam'iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.
A ranar 20 ga watan Maris na 2023 ne Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na jihar Kano.
Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

Comments

Popular posts from this blog

Ankai Sheikh Aminu Daurawa Bango Yayi Murabus Daga Kan Shugaban Hukumar Hisbah Na Jihar Kano