Sakamakon tashin gwauron zabbin kayan masarufi da ‘yan Najeriya ke fama da shi wanda matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta ya haifar, yanzu haka mutane da dama ba sa iya samun abinci sau uku a kullum.
Bayanai sun nuna cewa su kansu wadanda suke samun ukun a kowace rana, sun sauya daga abin da suka saba ci a baya zuwa mai sauki wanda za a saya da kudi kadan sannan kuma zai cika ciki.
Daga bayanai da kuma binciken da BBC ta yi a kasuwanni, ga wasu jerin abinci ko kuma kayan hadin abinci guda bakwai da yanzu jama’a suka sauya domin samun sa’ida:
Shinkafa: Yanzu haka magidanta da dama sun koma amfani da wata nau’in shinkafa da ake wa lakabi da “A Fafata”. Ita wannan shinkafar dai ta yi kama da wadda a zamanin baya lokacin wadata ake kira “dameji” wato wadda kamfani ya fitar saboda ta lalace. Bayanai sun nuna ana sayar da kwanon irin wannan shinkafa ta “A fafata” naira dubu biyu da dari biyar.
Garin Samanbita zuwa garin alabo: Yanzu haka shi ma garin samanbita da aka fi da “semovita” ya zama ba duk gida ba saboda yadda farashinsa ya yi tsahin gwauron zabbi, inda ake sayar da kwara guda daya a kan naira 1,300, inda shi kuma buhun ake sayar da shi a kan 11,000. Hakan ne ya sa masu karamin karfi karkata akalarsu zuwa garin alabo saboda ya fi saukin farashi. Harwayau, bayanai sun nuna da dama ma magidanta kan auni hatsi – masara ko gero ko dawa su wuce kai tsaye zuwa wurin nika ba tare da an surfa wato jama’a na cin abin da Hausawa ke kira “datsa”.
Dankalin turawa zuwa na Hausa: Sakamakon yadda farashin dankalin turawa da aka fi sani da “Irish” ya wuce tunanin talaka, ya sa a kasuwanni yanzu haka ake ta rububin dankalin gida ko kuma “sweet potato” da turanci. Ana dai sayar da kwandon dankalin turai a kan naira 5,000, yayin da shi kuma dankalin na gida ko kuma na Hausa ake sayar da shi a kan kudi naira 1,500.
Tumaturi zuwa gwalagwaji: Bayanai sun nuna yadda masu kayan gwari ke yin tanadin tumatur irin wanda ake kira gwalagwaji sakamakon tsadar da danyen tumatur ya yi a kasuwa.
Shayi ruwan bunu: Saboda tsadar madara, yanzu jama’a da dama kan amfani da ganyen shayi ne zalla domin hada shayin da Bahaushe yake kira “ruwan bunu”.
Dan zaki maimakon Sukari: Tsadar sukari ta sa ‘yan Najeriya da dama yin amfani da nau’in wasu abubuwan da ke zakaka abinci ko abin sha.
Miya babu nama: A baya dai watakila mutane da dama su ji kunyar fito da tuwo ko abincin gidansu idan babu nama a cikinsa saboda irin wadatar da ake da ita. Amma a yanzu musamman sakamakon tsaninin rayuwar da ‘yan Najeriya suka shida, ba koyaushe ake yin miya da nama ba.
To sai dai yayin da ‘yan Najeriyar ke tafiyar da wannan sauyi, masana na cewa hakan yana da amfani da kuma illa. Misali babu tabbas na ingancin shinkafar da ake kira ‘A fafata’ kasancewar masu amfani da ita ma sun ce ba ta kwana idan aka dafa ta.
Batun sanya dan zaki a abinci ko abin sha shi ma wani abu ne da masana harkar lafiya kan ja hankalin jama’a da su guji yin hakan.
Sauran sauye-sauyen kuma kamar shan shayi babu madara da amfani da alabo maimakon semovita da yin amfani da dankalin gida maimakon na turawa da kuma amfani da tumatur gwalagwaji duk ba su da illa. Sai dai kawai a ce iya kudinka iya shagalinka
Comments
Post a Comment