Zargin Sace Wayar Madagwal Da Madam Korede Tayi/G Fresh Ya Musanta Maganar Bashi Da Lapiya

Image
A Ranar Lahadi Babban Kaftin Na Nijeriya Ahmad Musa Ya Hada Wani Wasan Kwallon Kafar Na Manyan Sanannu A Arewa Domin Yin Zumunchi Inda Jaruma Da Manyan Celebrate Da Suka Hada Da Ali Nuhu, Umar M Sharif Madagwal ,Madam Korede Da Dai Sauransu Suka Halirchi Wajen PLAY ▶️ Saide A Yayin Da Aka Kammala Taron Ne Sai Wata Magana Ta Fito Ta Bakin Madagwal Inda Ya Bayyana Cewar Madam Korede Ta Sace Masa Waya A Yayin Da Suke Cin Abinchi Bayan Kammala Wasan Nasu Amma Nata Bangaren Madam Korede Ta Karya Batun Inda Ta Musanta Abun Har Abun Yakai Su Ga Zuwa Ofishin Yan Sanda Don Neman Hanginsa Da Yayi Kirarin Ta Tauye Masa Madagwal Ya Bayyana Hakane A Tattaunawa Sa Da  Freedom Radio Har Ya Bayyana Musu Yadda Abun Ya Faru Da Kuma Matsayar Kas Din Nasu Inda Yace Tun Fara Sun Sami Matsala Ne A Kwanakin Baya Da Madam Korede Inda Daga Bisani Ya Bashi Hakuri Har Allah Ya Kawo Wannan Taron Suka Hadu Da Ita Take Bibiyar PLAY ▶️ Yace A Lokacin Da Suka Kammala Wasan Shi Kuma Da Kaya...

An aikewa majalisar dokoki takardar neman rushe Masarautu hudu da dawo da Sunusi Sarkin Kano

Yanzu haka wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rushe dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta gabata ta kafa, tare da neman a maido da Sarkin Kano na 14 Mallam Muhammadu Sanusi II.

Dala fm na ruwaito,bayanin kungiyar na zuwa ne ta cikin wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024, da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, inda ta ce rusa masarautu tare da maido da Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar Kano.

Jaridar Kadaura24 ta rawaito cewa rubutun wasikar na cewa:
“Mun rubuto wasikar ne don rokon wannan majalisar da ta yi gyara a dokar masarautun jihar kano, muna so a gyara dokar ta yadda za’a rushe sabbin masarautun da aka kirkira guda hudu a shekarun baya.

Wasikar ta ci gaba da cewa, “Mun yi imanin idan har aka hade masarautun suka koma masarauta daya za’a fi samun hadin kai da ci gaban al’ummar Kano”.

“Kuma rushe masarautun gusa hudu zai inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar kano, don haka muke neman wannan gida zai yi abun da ya da ce dai-dai da doka”.

Wasikar ta kara da cewa, “Mun amince da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke da shi kan harkokin tafiyar da masarautu”.

“Duk da haka, cikin kaskantar da kai muna rokon majalissa da ta sake duba matakin tsige Sarki Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki da akayi a baya, Imaninmu ya ta’allaka ne a kan cewa mayar da shi kan karagar mulki za ta samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano, “in ji wasikar”

Comments

Popular posts from this blog

Ankai Sheikh Aminu Daurawa Bango Yayi Murabus Daga Kan Shugaban Hukumar Hisbah Na Jihar Kano