Wasu daga cikin shawarwari waɗanda za a iya amfani da su don yin ƙoƙarin rage aikata istimna'i ko barin sa gaba daya:
■ Da farko dai tsoron Allah shine akan gaba, idan baka dubi darajar dokar Allah daya saka maka ba yace kada ka ƙetara, to kaji tsoron tsoron damages din dazaka jawowa jikin ka.
■ Allah Madaukakin Sarki wanda shi ya halicci dan Adam, yafi kowa sanin halin dan Adam, ya riga ya baka mafita acikin Alqur'aninsa mai tsarki. Yace wa Annabinsa (S.A.W).
"Ka gaya wa muminai maza su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu. Yin haka shine yafi tsarkakewa garesu, Hakika lallai Allah masani ne game da abinda suke aikatawa".
■Manzon Rahama (S.A.W) yace :
"Yaku samari! Wanda yake da ikon rike iyali (ko ikon biyan bukatar jima'i da iyali) daga cikinku, to lallai yayi aure. Domin yin hakan shi yafi sanya runtsewar idanu kuma yafi katangewa ga al'aura.
■ Yawan yin addua da karatun Al qur'ani da yin ibada akan lokaci da sauran abubuwan da zasu kara maka kusanci da Ubangijin ka.
■ Sarrafa lokutan da kuke jin sha'awar aikata istimna'i idan yazo muku;
Hakan na faruwa ne ta hanyar yin duk wani abin da kuka san zai janye muku tunani daga wannan sha'awar data taso maka, kamar shiga cikin jama'a ayi hira, wasannin game, ko duk wani aiki kamar tafiyar kafa, jogging da sauransu.
■ Ƙayyade yawan lokacin da kake aikata istimna'i:
Kana iya dainawa a hankali a hankali ta hanyar dakatar da yawan aikata istimna'i alal misali, za ka fara da kauracewa aikatawa na tsawon kwana uku, sannan daga nan zuwa mako guda, ko wata wata har Allah ya taimakeka ka daina.
■ Ware lokaci mai yawa da zaka kasance tare da abokai da yan'uwa acikin wuni shima zai taimaka wajen dauke tunanin ka daga aikata wannan mummunar dabi'a.
■ Kauracewa kallon finafinan batsa.
■ Ka yi ƙoƙari ka kauracewa abokan da suke aikata istimna'i ko masu yawan yin magana akan istimna'i.
■ Idan kana cikin masu matsalar aikata istimna'i yayin da kake cikin bandak, yi kokarin kayyade yawan lokacin da kake diba a bandakin ta hanyar saita alarm na ɗan gajeren lokaci kuma kayi ƙoƙarin fita kafin lokacin ya cika.
■ Ka kauracewa yawan zama akan gadonka ko katifa, kayi amfani da tebur ko kujera, sannan ka tabbatar da cewa kana zama cikin mutane a koyaushe.
■ Ka guji taɓa sassan jikinka da kan saka jin daɗi a yayin da sha'awar jima'i tazo maka.
■ Yi ƙoƙarin daina yin barci da wuri, kayi kokarin yin wasu al'amuran kamar su karatun littafi, hakan yana rage sha’awar yin su.
■ Daga karshe, ba zai yiwuba kana kalle-Kallen haramun sannan kace sha'awa ba zata rika damunka ba.
Don haka kaji tsoron Allah ka runtse idanuwanka daga kallon duk abinda Allah ya haramta gareka.
ALLAH YA KAREMU.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam
Comments
Post a Comment